• Labaran yau

  Girgizar kasa ta rutsa da masu hawa tsauni 200

  Sama da masu hawa dutse 200 ne suka makale a kan wani dutse a wani tsibirin yawon bude ido na kasar Indonesiya, Lombok, bayan wata mummunar girgizar kasa ta haddasa zaftarewar kasar da ta yanke hanyoyin tserewa.

  A halin yanzu daruruwan masu aikin ceto suna kokarin kubatar da su daga dutsen Rinjani, wani wurin hawa dutse mai farin jini.

  Girgizar kasar mai karfin maki 6.4 ta afku ne da sanyin safiyar Lahadi kusa da karkashin dutsen.
  A kalla mutum 16 sun mutu, kuma sama da mutum 160 sun jikkata a girgizar kasar.

  Jirgi mai saukar ungulu da kuma masu aikin ceto da ke tafiya a kasa suna hawa dutsen da suka makale a gefen dutsen.

  Su wa abin ya shafa?

  Dubban gidaje ne dai suka lalace kuma daruruwan mutane suka rasa muhallansu yayin da motsin kasar da ta biyo bayan girgizar kasar ta girgiza Lombok da kuma Tsibirin Bali mai makwabtaka.

  Wani mai yawon bude ido dan kasar Malaysiya wanda yake yawon hawa dutse a Rinjani, yana cikin wadanda suka mutu.

  Wani matashi dan Indonesiya mai hawan dutse ma ya mutu bayan duwatsu sun fado masa a kai.
  Masu hawan dutse daga Faransa da Thailand da Netherlands da kuma Malaysiya suna cikin wadanda suke jiran a ceto su daga Mount Rinjani.

  Hukumomi sun ce sama da mutum 500, yawanci masu yawan buda ido daga ketare, sun riga sun sauko daga dutsen amma har wa yau mutum 266 suna nan a makale a wurin.

  Jirage masu saukar ungulu suna nan suna neman wadanda suka makale din.

  Wani jagoran masu yawon bude idanu, mai suna Sukanta, ya bayyana yanayin da wadanda ke kan dutsen har yanzu ke ciki.

  Ya ce: "Wasu daga cikin mutanen [sun kasance a] tafkin, domin tafkin na tsakiyar... ba za su iya tafiya ko ina ba domin zaftarewar kasa... Dole su tsaya kusa a tafkin."

  A yanzu wasu 'yan Malaysiya masu yawon bude ido, sun kai tudun mun-tsira kuma za su bar Lombok ta hanyar jirgin sama ranar Litinin bayan sun nemi taimako ta Facebook tun daga farko.

  Shin an saba girgizar kasa a Indonesiya?

  Eh, ana girgizar kasa a Indonesiya domin tana gefen 'Da'irar Wuta' - kan layin da ake yawan samun girgizar kasa da kuma aman wuta da ya zagaye kewayen yankin Pacific.

  A shekarar 2004, wata babbar girgizar kasa a gabar tekun Aceh ta kashe sama da mutum 160,000 a Indonesiya kadai.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  BBC
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Girgizar kasa ta rutsa da masu hawa tsauni 200 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });