• Labaran yau

  Ya shiga gidan wata mata don sata, kofa ta rufe da shi daga ciki asiri ya tonu

  Bahaushe ya ce son banza ke sa Kurkuku cika, asirin wani barawo mai suna Elijah Nehemiah ya tonu bayan ya shiga gidan wata mata da karfe 11 na dare a rukunin gidaje na Ekpene Obo a jihar Akwa Ibom domin ya yi sata bayan matar ta tafi Chochi, shigarsa dakin ke da wuya sai gogan naka ya kulle kofa daga ciki.

  Kulle kofar ke da wuya sai naka ya farga cewa ashe hannu da ake kamawa a murda domin kofar ya bude ya karye kuma baya makale a jikin kofar,

  Shi dai barawo ya yi iyakar bincike ko zai gano inda aka ajiye hannun murdawa domin kofa ya bude amma ya faskara. Daga karshe dai barawo ya yi saranda har mai gida ta zo ta kama shi dumudumu washe gari da safe.

  Kamar yadda aka saba, barawo Elijah dai ya sha dan karen duka tare da tozarci, kafin daga bisani aka mika shi ga mahukunta.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ya shiga gidan wata mata don sata, kofa ta rufe da shi daga ciki asiri ya tonu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });