Wata mutuniyar kasar Amurka Catherine Bridges ta kafa tarihi
inda ta haifi yara 17 cikin awanni 29 a asibitin Indianapolis Memorial da ke
Amurka.
Dakta Jack Morrow likitan da ya karbi haihuwar matar ya ce,
a lokacin da Catherine Bridges ta fara haihuwa jariran na ta fitowa daya bayan
daya. Likitan ya bayyana haihuwar tata a matsayin abin tsoro inda yace yaa dade
banga irin wannan haihuwar ba a duniya.
Catherine Bridges da Maigidanta sun
dade tare amma ba su samu haihuwa ba, a shekarar da ta gabata ne dai suka
ziyarci wani asibiti a garin Rhodes Island don ba su shawarwari a kan yadda za
su iya samun karuwa.
An samu nasara a kan shawarwarin da Likitocin asibitin suka ba ma’auratan inda suka samu ’ya’ya maza 17 a jere masu kama da juna.
An dai rada wa jariran suna masu kama da juna wadanda suka
hada da: James da Jacob da Jarod da Jarbis da Jason da Jeffrey da Jeremy da
Jerome da Jesse da Jimmy da Joachim da Jonathan da Jonas da Joseph da Julian da
Jimbo da kuma Darth
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
hausa.naij.ng