• Labaran yau

  Wani basaraken al'ummar Igbo ya sha duka har ya mutu daga hannun matasan gari

  Wani basaraken gargajiya a Ogbosinne na karamar hukumar Nkanu ta yamma a jihar Enugu Igwe Stephen Nwatu ya mutu bayan ya sha dan karen duka daga jama'arsa ranar 11 ga watan Yuni.


  Bayanai sun ce lamarin ya faru ne bayan basaraken ya yi kokarin hana wasu jama'arsa wadanda ke son su je wajen wani taro da za su yi tare da Gwamnan jihar Ifeanyi Ugwuanyi..


  An yi zargin cewa lamarin ya kazamce bayan basaraken ya umurci dirabansa ya bi ta kan mutanen da motarsa, amma sai direban ya ki, kuma sakamakon haka ya yi kokari domin ya yi ribas da motar amma cikin kuskure sai ya take wani tsoho da hakan ya sa ya kare a kafa nan take.


  Bisa wannan dalili  sai matasa kimanin 200 suka afka wa basaraken, suka lakada masa mumunar duka, sakamakon haka aka garzaya da shi Asibiti inda nan take ya ce ga garinku.


  Yanzu haka 'yansanda na gudanar da bincike kamar yadda Kakakin hukumar 'yansanda na jihar ya shaida wa manema labarai.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani basaraken al'ummar Igbo ya sha duka har ya mutu daga hannun matasan gari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });