• Labaran yau

  Tonon asiri, wani mutum da wata mata sun makale bayan sun gama zina

  Wani abin al'ajabi ya faru bayan wadansu mazinata sun makale bayan sun gama zina a cikin Baraka Hotel ranar Juma'a 8 ga watan Yuni, 2018 a garin Kitale na kasar Kenya.

  Rahotanni sun nuna cewa mutumin da aka kama yana da aure kuma 'dan haya ne a gidan matar da suka makale tare bayan aikata zina.

  Haka zalika rahotun ya ce tun asali, matar wannan mutum ta sha zargin cewa akwai wata alaka ta soyayya tsakanin mijinta da wacce suke haya a gidanta wanda mijin ya sha musantawa.

  Sakamakon haka matar ta nufi wurin wani boka wanda ya bata asiri da ya sa mijinta tare da wacce suke haya a gidanta suka makale.

  Ala tilasas aka kira 'yansanda wanda suka sha da kyar wajen shawo kan jama'a da suka yi cincirindo domin gane ma idanuwansu yadda mazinatan suka makale, duk da haka fa sai da 'yansanda suka dinga harbi a sama domin jama'a su watse.

  Daga karshe dai an warware mutanen a wani waje mai sirri, yayin da matar kunyataccen miji ta shigar da karan wacce suke haya a gidanta bisa tuhumar sace zuciyar mijinta sanin cewa yana da aurenta.

  Kalli bidiyon yadda lamarin ya kasance:  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tonon asiri, wani mutum da wata mata sun makale bayan sun gama zina Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });