• Labaran yau

  Kebbi: Buhari na gina wani katafaren madatsan ruwa domin kare gonakin manoma a gundumar Aljannare

  Isyaku Garba | Aljannare | 27-6-2018


  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da kwangilar gina madatsar ruwa a Tungan Rimi da kewaye a Gundumar Aljannare da ke karamar hukumar Suru a jihar Kebbi.

  Tuni dai aikin ya yi nisa kuma an kusa kammala kwangilar gina wannan madatsar ruwa.
  Cigaba da aikin datse ruwa


  Shi dai wannan madatsar ruwa zai zama kariya ga ambaliya da kogin Niger ke yi kusan kowane shekara wanda hakan yake haifar da barnar amfanin gona na milioyin naira ga manoma sakamakon mamaye shinkafa da ambaliyar ruwan ke yi.

  Tawagar Seniora News wacce ta kunshi kebbi24.com da isyaku.com sun ziyarci wajen da aikin ke tafiya inda aka ga aiki ya yi nisa, kuma bayanai sun nuna cewa ana sa ran kammala aikin nan ba da dadewa ba.
  Alh.Abubakar Saddik, Sarkin Sudan na Aljannare

  Sarkin Sudan na Aljannare Alh. Abubakar Saddik Dakingari, ya shaida mana cewa wannan babban alkhairi ne shugaban kasa ya yi wa kasar Aljannare, kuma sakamakon haka, ya ce " Amadadin jama'a ta ta kasar Aljannare da kewaye, ina mika godiya ta ga Shugaban kasa Muhamadu Buhari da ya kula da al'ummar Aljannare ta hanyar bayar da umarni domin a gudanar da wannan aiki.

   Haka zalika ina mika godiya ta ga Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da ya yi tsaye domin ganin wannan aiki ya tabbata, wannan ya nuna yadda wadannan shugabanni suke kula da lamarin talakawa, har da na Aljannare. Mun gode kuma Allah ya taimake su".
  Datse ruwa bangaren rafin Niger

  Sarkin Sudan na Aljannare ya kara da cewa, yanzu haka idan Allah ya yarda, suna kyautata zaton cewa jama'ar wannan karkara za su iya yin noman shinkafa sau uku a shekara daya, ganin cewa dama can ambaliyar ruwa ne daga kogin Niger ke zama barazana ga aikin noman shinkafa.

  Amma ganin cewa yanzu an samar da wannan madatsar ruwa, kenan manoma za su saki jiki domin su yi noma.

  Binciken mu ya nuna cewa, manoma da suka karbi bashi na anchor borrower a can baya suka sayi iri suka shuka, kuma bayan shinkafa ta tsiro ta yi kyau, sai ruwa suka zo daga kogin Niger suka yi ambaliya suka mamaye shikafar manoma a wanna karkara da kewaye, sakamakon haka ya haifar da dimbin assara domin shikafar ta mutu gaba daya.
  Wasu manoma a Tungar Rimi
  Sakamakon haka ya haifar da matsala wajen biyan kudin da manoman suka ara domin aikin shinkafa.

  Amma wannan madatsar ruwa yanzu, zai bayar da kariya ga irin wannan ambaliyar ruwa da zai haifar da yanayi ingantacce, wanda zai wadatar da ruwa a lakacin da ake so a sako su ba tare da sun zarce sun yi ambaliya ga amfanin goda ba.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Buhari na gina wani katafaren madatsan ruwa domin kare gonakin manoma a gundumar Aljannare Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });