• Labaran yau

  Maigida, matarsa da 'ya'yansu 3 sun mutu a daren farko da suka tare a sabon gidansu

  Wani ibtila'ia ya faru a kan wani iyali bayan 'yan gidan gaba daya da suka hada da mahaifi,mahaifiya 'yaya uku tare da wani abokin mahaifin suka mutu da dare bayan sun koma sabon gidansu a unguwar Aiyepe a yankin Sagamu na jihar Ogun ranar Laraba.

  Wani abokin mai gidan ya ce mamacin mai sana'ar gina rijiyar burtsatse ne kafin aukuwar lamarin , kuma ana zargin cewa an yi amfani da wani sinadari mai guba wajen pentin gidan.


  Majiyarmu ta ce an gano mutuwar wadannan mutane ne bayan an ji wani wari yana busowa daga gidan ranar Alhamis.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce rundunar tana gudanar da bincike a kan lamarin.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Maigida, matarsa da 'ya'yansu 3 sun mutu a daren farko da suka tare a sabon gidansu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama