• Labaran yau

  Kotun shari’ar musulunci ta garkame wani kwarto da ya sace zuciyar wata matar aure


  A yau, Alhamis, ne wata kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a magajin gari, jihar Kaduna, tayi umarnin a garkame wani mutum, Abubakar Mustapha, bisa zargin sad a sace zuciyar wata matar aure tare da karkatar da hankalin ta daga kan mijin ta. 

  Mustapha ya musanta cajin da ake tuhmar sa da su a gaban kotun. Neman matar aure ya saba da sashe na 226 na kundin tsarin shari’ar fenal kod na jihar Kaduna da aka kirkira a shekarar 2002. 

  Saidai kotun karkashin mai shari’a, Malam Musa Sa’ad, bata gamsu da musanta zargin da Mustapha ya yi ba, hakan ya saka tayi umarni a cigaba da tsare shi a wurin ‘yan sanda har sai an cimma matsaya dangane da bayar da belin sa 

  Tunda farko, mai kara; mijin matar, Yusuf Sadi, ya shaidawa kotun cewar matar sat a hadu da kwarton ne tun bayan da ta tafi gidan su a Kafanchan domin haihuwa amma kuma ta ki dawowa gida bayan haihuwar ta. Sadi ya sanar da kotun cewar, Mustapha ya taba kiran sa a waya tare da neman ya saki matar sa, Nusaiba domin yanzu ba matar sa ba ce. 

  Kazalika ya shaidawa kotun cewar, “lokacin da na bi sahun mata ta domin dawo da ita gida sai Mustapha ya kira ta zuwa dakin sa, ganin ta tafi sai na bi bayan ta amma da muka isa dakinsa sai ya daka min tsawa tare da fada min cewar ya kira mata ta ne ba ni ba.” Sadi ya roki kotun da ta takawa Mustapha birki tare da bukatar ta saka baki domin matar sat a dawo gidan sa.
   
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com 

  hausa.naij.ng
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Kotun shari’ar musulunci ta garkame wani kwarto da ya sace zuciyar wata matar aure Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama