• Labaran yau

  Kebbi: 'Yan fashi sun sace kudaden albashin kananan hukumomi 3 - ISYAKU.COM

  Yan fashi sun yi awon gaba da kudaden albashi na kananan hukumomi guda uku, Gwandu,Birnin kebbi da Suru.

  Daily Sun ta ruwaito cewa 'yan fashin sun sace kimanin N9m kudaden albashin karamar hukumar Gwandu, kimanin N1.655m na ma'aikatan Gwamnati a Birnin kebbi, sai karamar hukumar Suru da ba a san adadin kudaden da 'yan fashin suka sace ba.

  Rahotu ya nuna cewa 'yan fashin sun biyo mai biyan albashi na karamar hukumar Gwandu ba tare da saninsa ba, bayan ya fito da kudin daga Banki kuma ya nufi gidansa . Amma yayin da ya tsaya domin ya bude get na gidansa sai 'yan fashin suka yi masa diran mikiya suka yi awon gaba da motar wadda take dauke da kudin.

  Kusan lokaci daya sauran 'yan fashin suka dira a Birnin kebbi da Suru yayin da suka aikata aika aikan.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Kebbi: 'Yan fashi sun sace kudaden albashin kananan hukumomi 3 - ISYAKU.COM Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama