• Labaran yau

  Kalli yadda wani mugun 'dansanda ya mari matar aure da ke shayar da jariri

  Yayin da 'yansanda kirki ke kokarin kare lafiyar 'yan Najeriya, shi kuma wani mugun 'dansanda mai suna Kehinde Agbede ya huce haushin sa ne a kan wata matar aure wacce ke goye da jariri. Shi dai wannan 'dan dambe da mata a cikin kakin 'dansanda ya zare hannunsa ne ya kwada ma wannan matar mari duk da yake matar tana 'dauke da goyon jariri.

  Wannan lamari ya faru ne a unguwar Makolo da ke birnin Ibadan. Bayanai sun ce laifin matar shine kawai domin ta shawarci 'dansandan cewa kada ya jawo hadari a kan hanya saboda N50 bayan ya tsayar  da 'dan acaba da ya goyota a tsakiyar titi.

  Jin haka ke da wuya sai gogan naka ya fusata kuma ya waska ma wannan mata mari wanda ya sa hannayen yatsun sa suka bayyana a fuskar matar.

  Bayanai sun ce shi wannan 'dansanda yana aiki a ofishin 'yansanda na Makolo da ke birnin Ibadan.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli yadda wani mugun 'dansanda ya mari matar aure da ke shayar da jariri Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });