• Labaran yau

  Hotunan yadda mutum 9 da motoci 53 suka kone kurmus sakamakon gobarar wata tankar man fetur

  Hukumar bayar da taimakon gaggawa na jihar Lagos LASEMA ta ce mutum 9 ne suka mutu yayin da motoci 53 suka kone sakamakon wata gobara da ta tashi bayan wata tankar man fetur ta yi bindiga a unguwar gadar Otedola da ke birnin Lagos ranar Alhamis.

  Shuban hukumar ta LASEMA Adesina Tiamiyu ya shaida wa PM News cewa motar tankar ta fadi ne misalin karfe 5:53 na yamma, daga bisani ta yi bindiga sakamakon haka motoci da ke bayanta suka kama da wuta gaba dayansu.

  Ya ce mutum tara sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane su ba, amma an ceto mutum hudu, biyu a cikin mawuyacin hali yayin da ragowar biyu ke da raunuka da basu da muni.

  Ya kuma ce, gaba daya dai motoci 53 ne suka kone yayin da yake nuna tausayi da bakinciki a kan wannan lamari.

  Jami'an LASEMA,FRSC da LATSAM ne suka yi ta kokarin ceton jama'a a wajen wannan gobara, yayin da sauran jama'a ke taimakawa domin a kawar da ragowar garwar motar tankar tare da sauran motoci da suka kone daga hanya.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotunan yadda mutum 9 da motoci 53 suka kone kurmus sakamakon gobarar wata tankar man fetur Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });