• Labaran yau

  Hotuna: Allah wadai mai kisa, kalli wanda ya kashe budurwarsa don tsananin kishi

  Muhammed Adamu 'dan shekara 30 wanda ya ce shi 'dan kwaya ne, ya kuma amsa cewa shi ne da kansa ya kashe budurwarsa Hauwa Muhammed 'yar shekara 24 a garin Damaturu na jihar Yobe.

  Kwamishinan 'yansanda na jihar Yobe CP Abdulmalik Sumonu ya shaida wa manema labarai haka a Damaturu, ya kuma ce Muhammed ya bayar da jawabinsa inda ya amsa cewa shi ne da kansa ya kashe Hauwa.


  Muhammadu ya kashe budurwarsa Hauwa bayan ya kasa fitowa domin aure sakamakon haka Mahaifinta ya bukaci ta fitar da wani, bayan wani ya fito kuma aka yi na'am da shi a gidansu Hauwa sai Muhammadu ya shiga tekun bakinciki sakamakon haka ya aika Hauwa bakoncin Lahira.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Hotuna: Allah wadai mai kisa, kalli wanda ya kashe budurwarsa don tsananin kishi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama