• Labaran yau

  Girma ya fadi, an kama tsoho yana sa kayan asiri a cikin filin wani saurayi

  Rashin dogara ga Allah da tawakkali ya kai wani tsoho cikin taskar da na sani, asirin wannan tsoho mai suna Francis Obidi ya tonu bayan an kamashi dumu dumu tare da wasu kayakin tsafi da asiri yayin da yake kokarin binne wadannan ababe a cikin Fili mallakar wani matashi.

  Wannan lamarin ya faru a kauyen Umuduru da ke Nempi a karamar hukumar  Oru ta yama a jihar Imo.

  Sakamakon haka aka zagaya da wannan tsoho a cikin kauyen dauke da wadannan kayakin asiri daga karshe aka kore shi gaba daya daga kauyen.


  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Girma ya fadi, an kama tsoho yana sa kayan asiri a cikin filin wani saurayi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama