• Labaran yau

  Ashsha, kalli yadda aka jaye wani mataimakin gwamna da karfi daga kujerarsa a wajen taron APC

  Daga Wakilin isyaku.com

  Rahotanni da muka samu daga birnin Abuja wajen taron jam'iyar APC na kasa ya ce mataimakin Gwamnan jihar Imo ya gamu da wulakanci a wajen taron bayan jami'an tsaron Gwamna Rochas Okprocha sun jaye shi daga kan kujerar da yake zaune a waajen taron domin wani daban ya zauna.

  Rudani ya fara ne bayan mataimakin Gwamnan jihar Imo tare da mukarrabansa wadanda basu ga maciji da Gwamna Rochas sun sami kujeri suka zauna a wajen da aka ware domin tawagar jihar Imo a wajen taron. Amma bayan isowar tawagar Gwamna Rochas, sai aka bukaci mataimakin Gwamnan  tare da jama'arsa su tashi amma sai suka ki.

  Sakamakon haka aka kira dogarawa, wadanda sune jami'an tsaro na Gwamna Rochas, suka zo suka ja mataimakin Gwamnan Eze-Madumere da karfi daga kan kujerar da ya zauna, haka zalika suka nufi wajen Hillari Eke shugaban banagaren da ke adawa da Gwamna Rochas duk aka jefar da su daga kan kujerarsu tare da magoya bayansu.

  Jam'iyar APC a jihar Imo ta aminta da Eke a zaman shugaban jam'iyar, lamari da ya jawo zaman doya da manja tsakanin Gwamna Okorocha da John Oyegun wanda shi ne tsohon shugaban jam'iyar na kasa. Sakamakon haka, 'ya'yan jam'iyar na jihar Imo suka fuskanci juna da yakin zafafar kalamai kuma wannan duka yana faruwa ne daidai lokacin da shugaba Buhari ke karanta jawabinsa a wajen taron.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ashsha, kalli yadda aka jaye wani mataimakin gwamna da karfi daga kujerarsa a wajen taron APC Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });