Biyan albashi kafin bikin Sallah, yadda Gwamna Bagudu ya sha buhun albarka

Daga Isyaku Garba | Birnin kebbi | 15/6/2018


Kamar ko'ina a Arewacin Najeriya da wurare da ke da al'ummar Musulmi, an gudanar da Sallar Idin karamar Salla a cikin garin Birnin kebbi da kewaye, haka zalika, Sallar Idin a babban Masallacin Idi  na jihar Kebbi wanda ke unguwar Gesse karkashin jagorancin Babban Limamin Masallacin Juma'a na Fadar Sarkin Gwandu ya sami halartar Gwamna Atiku Bagudu, Ministan shari'a Abubakar Malami tare da sauran hadiman Gwamna Bagudu.

Mai Martaba Sarkin Gwandu tare da jama'arsa, 'manyan 'yan kasuwa,'yan siyasa tare da dubban jama'a suka halarci Sallar Idin.

Wani jin ra'ayin jama'a daga Mujallar ISYAKU.COM ya nuna cewa wannan Sallar an yi shi cikin jin dadi da walwala, sakamakon albashi da Gwamna Atiku Bagudu ya biya na watan Yuni duk da cewa watan bai kare ba, wanda haka  ya haifar masa da farin jini tare da addu'oi na Allah ya kiyaye daga yawancin ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi.

Tun ranar jajibirin Sallah garin Birnin kebbi ya dauki haraman jama'a, ganin cewa wadanda ke aiki ko zaune a wurare kamar Abuja,Kaduna Lagos da sauransu sun dawo gida domin gudanar da bikin Sallah karama.

Har zuwa karfe biyu na daren Sallah  ana ta hada hada sakamakon yadda aka gan mata da yara a kasuwannin baje koli na hanyar tsohuwar Mayanka, yayin da shagunan sayar da kayan yara suka kasance a bude domin jama'a na ta kai kawo.

Bangaren dabbobi kuwa, Mujallar ISYAKU.COM ya kula cewa Kaji fa sun sha wuka, balle dabbobi kamar shanaye da sauransu wanda hakan ya kasance sakamakon samun albashin ma'aikata kafin Sallah karama.

Ko irin wannan tagomashi zai sa ma'aikatan jihar Kebbi su kara gamsuwa da salon shugabanci na Gwamna Atiku wanda bayan wannan, ya kuma dage tun hawansa mulki domin tabbatar da cewa ya biya ma'aikatan Gwamnatinsa albashinsu da zarar wata ya kare?. Lokaci ne zai tabbatar da haka.

Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN