• Labaran yau

  Ashsha, karanta abin da aka yi ma wannan saurayi bayan ya saci akuya mai juna biyu

   'Yan bangan Umuchiana a garin  Ekwulobia na karamar hukumar Aguata na jihar Anambra sun cafke wani fitaccen barawo da ya shahara wajen satan awakin makwabta bayan ya saci wata akuya mai juna biyu.

  Shi dai wannan barawo saurayi ne, kuma ya zo garin ne kawai domin ya yi sata kamar yadda ya saba.

  Haka zalika wannan barawo ya sace wata akuya a kauyen Okpo 'yan kwanaki da suka wuce. Amma a yayin da yake kokarin zuwa wajen mai sayen awakin da yake satowa a Ezinifete, sai 'yan banga suka cafke shi a hanyar COC.

  Gogan naka dai ya daku, aka wulakanta shi, kuma aka daura masa wannan akuya aka zagaya da shi cikin gari domin ya zama izna ga suran mutane.

  ZIYARCI SENIORA TECH DOMIN FLASHING KO CIRE SECURITY NA WAYAR SALULARKA A GARIN BIRNIN KEBBI. SHAGO MAI LAMBA 50, HAWA NA SAMA DAGA GEFEN HAGU, YAMMA DA GIDAN MARIGAYI WAZIRI UMARU. TAUSHI PLAZA, TITIN AHMADU BELLO.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ashsha, karanta abin da aka yi ma wannan saurayi bayan ya saci akuya mai juna biyu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama