• Labaran yau

  Ana shirin takawa masu amfani da Facebook, Twitter, instagram burki a Majalisa


  Majalisar Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa masu amfani da Facebook da Twitter da irin su Instagram da dai sauran shafukan sada zumunta na zamani za su gamu da wasu sauye-sauye daga Gwamnati.

  Shugaban kwamitin na’urori na zamani a Majalisa watau ICT Sanata AbdulFatai Buhari ya bayyana cewa ‘Yan Najeriya na cin zarafin kafofin na zamani su na yin abin da ya wuce gona da iri don haka dole a taka masu burki.

  Sanata Buhari ya bayyana wannan ne wajen wani taro da aka yi kan mau barna a shafukan gizo a babban Birnin Tarayya Abuja. ‘DanMajalisar Dattawan yace idan aka rabu da ‘Yan Najeriya su na iya jefa kasar cikin wani rikici.

  Sanatan ya bayyana cewa wasu a Kasar na yada labaran da ba dai-dai bane saboda kokarin ganin bayan ‘Yan adawar su na siyasa. Don haka ne dai aka kawo kudirin da zai kawo gyara a gaban Majalisan kasar kuma har batun yayi nisa. Daily Trust ta rahoto cewa Ministan sadarwa na Kasar Adebayor Shittu dai yace Ma’aikatar sa za su hada kai da Ofishin mai bada shawara kan harkokin tsaro da kuma Majalisa domin maganin masu yada labarai na bogi a kafofin sadarwan.
   
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  hausa.naij/ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ana shirin takawa masu amfani da Facebook, Twitter, instagram burki a Majalisa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });