• Labaran yau

  An yi wa 'dansanda da ya harbi jama'a a Ekiti koran kare daga aikin 'dansanda

  Rundunar 'yansanda na jihar Ekiti ta ce an yi wa 'dansanda da ya yi harbi da bindiga a lokacin taron jam'iyar APC a Ekiti koran kare daga aikin 'dansanda. Ranar Juma'a da ta gabata ne 'dansandan ya yi harbi da ya yi sanadin raunata wani 'dan Majalisa Opeyemi Bamidele tare da wadansu mutum biyar.

  Kwamishinan 'yansanda na jihar Ekiti Bello Ahmad ne ya tabbatar wa manema labarai haka yana mai cewa rundunar ta yi haka ne domin ta kare martabarta.

  Bayanai sun nuna cewa korarren 'dansandan yana aiki da Mopol 20 da ke Lagos, amma ya zo Ekiti wajen aikin bogi kafin tsautsaye ya fada masa kuma sakamakon haka ya sami tukuicin koran kare daga aikin 'dansanda ba pansho balle gratuti wai kato yayi aikin banza ba godiya kenan.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An yi wa 'dansanda da ya harbi jama'a a Ekiti koran kare daga aikin 'dansanda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama