• Labaran yau

  An gano wajen da ake wanke gurbataccen shinkafa sai a sake durawa a buhu domin a sayar wa jama'a

  Ya zama wajibi masu amfani da shinkafa su kula da irin shinkafar da zasu saye sakamakon yadda hukumar da ke kula tare da kare hakki masu amfani da abinci da sa ido a ingancin abinci na Najeriya CPC ta bankado wata chakwakiya inda ake sarrafa gurbataccen shinkafa kuma a sake loda su domin a sayar wa mabukata. An gano wadannan wurare ne a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

  Bayanai sun ce an yi odan gurbataccen shinkafar ne daga kasar waje, inda aka saka su a wata masana'anta, kuma daga nan sai a wanke shinkafar sai a busar a rana, bayan shinkafar ta bushe sai a sake sakawa a cikin buhu domin a sayar wa jama'a.

  Wani 'dan jarida da ke aiki da AIT, Idongesit Ikono, wanda ke cikin tawagar jami'an CPC da suka kai samame a wasu shaguna da ke unguwar Nyong Essien da wani fitaccen shago a titin IBB a cikin Uyo
   ya ce "duk wata shinkafa a birnin Uyo wacce ta fito daga Mama Gold, Cap Rice, Stallion Rice da ke zagayawa a kasuwa duk gurbatattun shinkafa ne da aka wanke aka busar daga bisani aka sake durawa a buhu domin sayar wa jama'a".

  Ya kara da cewa "CPC ta ce an haramta shigowa da wadannan shinkafa tun 2015 a Najeriya".

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An gano wajen da ake wanke gurbataccen shinkafa sai a sake durawa a buhu domin a sayar wa jama'a Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });