• Labaran yau

  Allah ya tona asirin jami'in 'dansanda da ke tafiyar da gungun 'yan fashi da makami

  Wani jami'in 'dansanda mai suna Sgt. Ndubuisi Okoro ya fada hannu bayan an kama shi sakamakon aikata fashi da makami da satar mutane domin karbar kudin fansa. Sgt. Ndubuisi shi ne Odale watau babban dogarin Kwamandan jami'in 'dansanda na SARS mai kula da ayyukan fashi da makami a jihar Rivers.

  Haka zalika 'yansanda sun kama wani jami'in SARS Sgt. Christopher Abakpa bisa zargin aikata fashi da makami da satar jama'a.
   
  Scannews ta ruwaito cewa wadanda aka kama suna gudanar da wata kungiya ta mutum 8 wadanda jami'an 'yansandan suka 'daure ma gindi suna aikata fashi da makami tare da satar mutane domin karban kudin fansa a jihar Cross Rivers.

  Yanzu haka an kama wa'dannan 'bata garin 'yansanda kuma ana tsare da su a ofishin SARS a birnin Port Harcourt yayin da ake shirye shiryen mika su ga hedikwatar 'yansanda a birnin Abuja domin ci gaba da bincike.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Allah ya tona asirin jami'in 'dansanda da ke tafiyar da gungun 'yan fashi da makami Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });