• Labaran yau


  Abuja: Shari'ar jihar Kebbi, Bangarori da lamarin ya shafa sun halara, ana jiran shigowar Alkali

  Isyaku Garba | 29-6-2018


  Rahotanni da suka fito daga Kotun tarayya da ke birnin Abuja sun tabbatar cewa yanzu haka bangarori  da ke jayayya da juna a kan shari'ar kujerar Gwamnan jihar Kebbi a gaban Kotu sun kama wuri sun zauna daf suna jiran isowar Alkalin Kotun.

  Yanzu haka Lauya mai kare Gwamnatin jihar Kebbi Barr. Maikyau SAN da tawagarsa, Kwamishinan Shari'a ta jihar Kebbi Barr. Ramaru Gulma, kanin Gwamnan jihar Kebbi Ibrahim Bagudu tare da sauran jama'a sun halara a cikin dakin Kotun.

  Duk Lauyoyin bangarorin da lamarin ya shafa suna cikin dakin wannan Kotu, yayin da kowa ya sa ido domin ganin shigowar Alkalin Kotun, wanda kawo yanzu motarsa ta shigo harabar ginin wannan Kotu.

  Ku kasance tare da mu domin jin yadda za ta kasance a wannan shari'ar.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Abuja: Shari'ar jihar Kebbi, Bangarori da lamarin ya shafa sun halara, ana jiran shigowar Alkali Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama