• Labaran yau

  Zargi: Rudani a Port Harcourt bayan 'dansanda ya harbe hafsan soji da bindiga

  Ana fargaban abin da zai iya faruwa yayin da hankalin mutane ya tashi a Port Harcourt na jihar Rivers bayan an zargin cewa wani jami'in dansanda ya harbe wani hafsan soja a kusa da ofishin 'yansanda na Kala da sanyin safiyar yau.

  Duk da yake babu cikakken bayanin musabbabin aukuwar lamarin, amma wata majiya ta labarta cewa an sami wata zafafar muhawwara ne da ya kai ga harbi.

  Wani rahotu da bamu tabbatar ba ya ce yanzu haka soji sun mamaye wannan yanki na Kala yayin da ake ci gaba da bincike.

  Mazauna yankin sun yi ta gargadin jama'a a shafukan sada zumunta inda suke shawartar mutane su kaurace ma wannan unguwa na Kala kafin hankali ya kwanta.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zargi: Rudani a Port Harcourt bayan 'dansanda ya harbe hafsan soji da bindiga Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama