• Labaran yau

  Yawan wadanda 'yan bindiga suka kashe a Kaduna sun kai 45 - Hotuna

  Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna cewa yawan wadanda suka mutu a harin da 'yan ta'adda suka kai a kauyen Gwaska ranar Asabar sun kai 45 kamar yadda kungiyar sa kai domin tabbatar da tsaro na Birnin Gwari suka ambata.

  Bayanai sun ce 'yan bindigan su bi wadanda suka shirya domin su kare garin na Gwaska kuma suka kashe da yawa daga cikinsu wadanda suka hada da yara kanana.

  Wata majiya ta ce wadanda suka kai harin 'yan bindiga ne daga jihar Zamfara kuma sun shafe awa uku suna gudanar da harkaarsu kafin su koma cikin daji bayan sun banka wuta a gidaje da dama.

  Kakakin 'yansanda na jihar Kaduna Muhktar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai amma bai kara wani haske ba.


  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yawan wadanda 'yan bindiga suka kashe a Kaduna sun kai 45 - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama