• Labaran yau

  'Yansanda 3 sun mutu a artabu yayin ceton Kwara daga 'yan bindiga - Hotuna

  Wasu jami'an 'yansanda uku sun mutu sakamakon artabu da wasu 'yan bindiga a karamar hukumar Yabo da ke jihar Sokoto. Rahotanni sun nuna cewa 'Yansandan sun mutu ne sakamakon harbe harbe da ya kaure tsakaninsu da 'yan bindigan yayin da 'yansandan suka yi kokarin dakile satar wani Kwara 'dan kasar Syria.

  An ga wasu jami'an 'yansanda cikin alhini da bacin rai yayin da suka ga gawakin 'yan uwansu da aka kashe bayan an kawo su a cikin mota.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Sokoto Cordelia Mwawe bai tabbatar da mutuwar jami'an 'yansandan ba, amma ya ce 'yansanda da lamarin ya rutsa da su suna wani Asibiti inda ake kula da su.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yansanda 3 sun mutu a artabu yayin ceton Kwara daga 'yan bindiga - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama