• Labaran yau

  Yadda aka yi nasarrar cire tsiro a fuskar wani mutum

  Shekaru goma sha biyar da suka gabata wannan bawan Allah ya sami hadarin babur a kudancin Najeriya, sakamakon haka ya sami rauni a fuskarsa wacce daga bisani ta haifar da tsiro da ya rikide ya zama lamari na rashin lafiya.

  Haka ya haifar da kadaici da fargaba da mutane ke nuna masa har da kyama ganin yadda wannan tsiro ya canza kamannun sa.

  Amma a wani tiyata da aka gudanar a kan wannan tsiro, wannan bawan Allahah ya samu lafiya kuma fuskarsa ta koma daidai.

  Haka ya nuna cewa yana da kyau a gaggauta zuwa Asibiti matukar an gamu da matsalar lafiya da ba'a san kansa ba cikin lokaci.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka yi nasarrar cire tsiro a fuskar wani mutum Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama