• Labaran yau

  Yadda aka kammala taron Mahaddata Alqur'ani kan Ramadana a jihar Kebbi

  Kungiyar Alarammomi na mahaddata Qur'ani na jihar Kebbi sun kammala taron lakca na bana gabanin isowar watan Ramadana. An gudanar da taron mai taken "Marhaban da Ramadan" a masaukin shugaban kasa da ke garin Birnin kebbi.

  Malam Yusuf Abubakar Suru ya bayar da lakca a kan ababe da dama da suka hada da rashin ingancin amfani da wayar salula wajen sanar da ganin watan Ramadana tare da wadataccen sharhi a kan haka, kuskuren zartar da hukunci ko da laifi ya tabbata, Malam Yusuf ya ce Hukuma ce kadai ke da hurumin zartar da hukunci.


  Ya kuma kara da cewa wajibi ne a kawar da son zuciya wajen gina addini, tare da kira a kan cewa kada a dinga kutsawa a kan lamari da ba'a da wadataccen ilimi a kai musamman wadanda suka shafi addinin Musulunci.

  Haka zalika a nashi jawabi , wani jigo a kungiyar ta Alarammomi na jihar Kebbi Alh. Ibrahim Bayawa ya bayar da lakca ne akan falalar watan Ramadan, ya kara da cewa a watan Ramadan ne ake daure Shaitan, tare da yin kira cewa kowane Musulmi ya yi kokari ya yawaita aikata alkhairi a cikin watan Ramadan domin samun falalar da ce cikin watar.

  Isyaku Garba

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka kammala taron Mahaddata Alqur'ani kan Ramadana a jihar Kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama