• Labaran yau

  SARS sun tarwatsa 'yan fashi 20 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

  Wani fashi da makami da aka yi a garin Jere da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da sanyin safiyar Asabar ya yi sanadin mutuwar wani sajen na 'yansanda tare da wani mutum bayan 'yan fashi kimanin 20 sun tare hanya da misalin karfe 6:00 na safe suna aikata fashi ga fasinjan motoci.

  Majiyarmu ta labarta mana cewa bayan jami'an 'yansanda na SARS sun isa wajen da lamarin ke faruwa ne sai harbe-harbe ya kaure tsakanin 'yan fashin da 'yansanda sanadin da ya sa albarushi ya sami sajen na 'yansanda tare da wani fasinja.

  Yayin da haka ke faruwa ne sai wata mota da ke tafe ta sami hadari a kusa da wajen da aka yi fashin inda nan take mutum hudu suka mutu goma suka sami raunuka.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: SARS sun tarwatsa 'yan fashi 20 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama