• Labaran yau

  Rigingimun cikin gida da zai iya ba jam'iyar APC mamaki

  Jam'iyar APC wacce ta maka jam'iyar PDP a kasa a zaben  2015 tana fuskantar jarabawar cikin gida da idan an ci gaba da kawar da ido za ta iya faduwa wannan jarabawar. Sakamakon haka kuwa shi ne gazawa ga mataki na ci gaba bisa lissafin cigaban karatun siyasa.

  Idan muka waiwaya baya, jam'iyar PDP ta fara samun matsaloli ne daga cikin gida wadanda suka samo asali daga korafe korafen danniya da aikata ba daidai ba ga manbobin jam'iyar.

  Marmakin shugabannin jam'iyar a waccan lokaci su mayar da hankali a kan koke koke da 'ya'yanta ke ta yi , sai shugabnninta tare da 'ya'yan jam'iyar masu rike da iko a waccan lokaci suka mayar da lamarin idan ala tilas ba za ka yi hakuri ba tau sai ka sasallami kanka daga jam'iyar.

  A lissafin wadannan mutane, ko ba da kai ba jam'iyar ta riga ta kafu ! kwatsam sai Allah ya ba wadannan mutane kunya a zaben 2015.

  Da yawa daga cikin su da suka canja sheka zuwa jam'iyar APC su ne suka ci zabe a APC kamar a jihar Kano tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Rabiu Kwankwaso.

  Da tafiya ta kankama sai halayen wasu ya fara baiyana na rashin hakuri da fahimta tare da mayar da hankali ga bukatun APC. Marmakin haka, sai suka dukufa domin ganin sun ci ma bukatun rayuwarsu marmakin kyautata wa al'umma da suka zabe su.

  Sakamakon haka lamarin ya rikide zuwa gaba tare da ganin laifin juna a cikin gida tsakanin 'ya'an jam'iyar APC. Misalin wannan shine gaba da ke tsakanin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da Sanata Dino Melaye wanda lamarin ya kai ga wulakanta Sanata Dino Melaye sakamakon zarginsa da yansanda suke yi da aikata laifi ga tsarin dokar Najeriya.

  A gefe daya kuma akwai rikicin siyasa da ta rikide zuwa babbar gaba mai munin gaske a jihar Kano tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Rabi'u Kwankwaso wanda ya kai ga bangarorin biyu suna kai wa junan su farmaki.

  Haka zalika sai kuma jihar Kaduna inda Gwamna Nasir El'rufai baya ga maciji da Sanata Shehu Sani wanda yan kwanakin kabaya Sanata Shehu ya amsa gayyatar jami'an 'yansanda a jihar Kaduna bisa zargin daure ma ayyukan bangan siyasa gindi.

  A jihar Kebbi kuma ,matsala ce ta cikin gida ta taso tsakanin 'ya'yan jam'iyar APC bangaren 4+4 da BBSO wadanda kungiyoyi ne guda biyu da ke da manufa iri daya na neman shugaba Buhari da Gwamna Bagudu na jihar Kebbi su sake tsayawa takara a zabe na 2019 amma sai aka sami banbancin ra'ayi wacce aka alakantawa da ko waye zai shugabanci tafiyar gaba daya a jihar Kebbi.

  Bisa lissafi, nazari da kididdiga kan yadda lamurra ke tafiya a siyasar jam'iyar APC a Najeriya, idan dai har ba an sami kwakkwarar kwamiti da zai shawo kan wadannan rigingimu da suka dabaibaye jam'iyar a cikin gida ba, lallai APC za ta iya fuskanci yiwuwar darewar mabiyanta da tuni wadannan rigingimu suka dama masu lissafi kamar yadda korafe korafen su ke zagayawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

  Daga Isyaku Garba.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rigingimun cikin gida da zai iya ba jam'iyar APC mamaki Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama