• Labaran yau

  Mutum 8 sun kone kurmus a gobarar tankar mai a Zing na jihar Taraba - Hotuna


  Rahotanni daga karamar hukumar Zing na jihar Taraba sun nuna cewa kawo yanzu mutum 8 ne aka tabbatar sun kone kurmus a gobara da ta tashi sakamakon karo da wadansu motocin tanka na man fetur suka yi.

  Haka zalika rahotun ya nuna cewa direban motar tankar yana gudun tsere wa wasu sojoji ne da suka biyo shi, sakamakon haka motar ta kwace mashi ta je ta yi karo da wata mota da ke tafe.

  Dalilin haka ne tankar ta fadi ta kama da wuta yayin da mai da ke cikin motar ya malala yanayi da ya haifar da bazuwar gobarar.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 8 sun kone kurmus a gobarar tankar mai a Zing na jihar Taraba - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama