• Labaran yau

  Mutum 1 ya mutu sakamakon artabu tsakanin mabiya Shi'a da 'yansanda a Abuja

  Wani rahotu da ya fito daga Abuja ya ce ana fargaban mutum daya ya mutu bayan wani artabu da aka yi tsakanin mabiya Shi'a da yansanda ranar Litinin.

  Rahoton ya kara da cewa mabiya Shi'a suna ci gaba da zanga-zanga ne a birnin na Abuja domin ganin cewa Gwamnati ta saki jagoransu Ibrahim Alzakzaky wanda ake tsare da shi a birnin Abuja.

  Rigimar wacce ta fi kamari a gaban babban Sakatariyar tarayya sakamakon haka ya haifar da cinkoso a wajen da ya shafi Majalisar tarayya da hanyar zuwa fadar shugaban kasa.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutum 1 ya mutu sakamakon artabu tsakanin mabiya Shi'a da 'yansanda a Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama