• Labaran yau

  Matar aure da saurayinta sun fada hannu sakamakon kashe diyar kishiyarta

  'Yansanda a jihar Niger sun kama wata matar aure 'yar shekara 15 mai suna Fatima Adamu tare da tsohon saurayinta Usman Muhammed sakamakon kashe diyar kishiyarta a kauyen Agbati na karamar hukumar Agae.

  Majiyar 'yansanda ta ce bayan Fatima da surayinta sun kashe Hauwa'u wacce mai gidanta ya haifa tare da tsohuwar matarsa, sai suka kai gawar cikin daji suka jefar kuma babu wassu sassa a jikin gawar.

  Fatima ta ce Hauwa'u bata aikata mata laifi ba kuma tana rokon a yi mata afuwa sakamakon wannan mugun aiki da ta aikata, haka zalika saurayin nata Usman shi ma ya yi nadaman aikata wannan danyen aiki.

  Rundunar 'yansanda ta jihar Niger ta ce za ta gurfanar da su a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matar aure da saurayinta sun fada hannu sakamakon kashe diyar kishiyarta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama