• Labaran yau

  Maigida ya kashe matarsa bayan ta ki ta dafa abincin dare

  Wata mata yar shekara 33 a garin Buguma na karamar hukumar Asari-Toru a jihar Rivers ta rasa ranta bayan mijinta ya fasa kwalba ya caka mata tsinin kwalbar a cinya bayan fada ya kaure a tsakaninsu saboda matar ta ki ta dafa abincin dare.


  Majiyarmu ta labarta mana cewa fada ya kaure ne bayan matar ta ki ta dafa abinci domin ta tafi wajen yin pati na zagayowar ranar haihuwarta tare da kawayenta,Bayan ta dawo da dare, maigida ya tunkare ta da zancen abinci sai lamarin ya rikide ya zama fada.

  Sakamakon haka matar ta rasa ranta domin jini da ya zuba da yawa daga jikin ta.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Maigida ya kashe matarsa bayan ta ki ta dafa abincin dare Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama