• Labaran yau

  Kotu ta daure wani matashi sakamakon cin amanar budurwarsa a Facebook

  Wata babban Kotun tarayya a birnin Maiduguri na jihar Borno ta daure wani matashi mai suna Ikechukwu Elom bayan ta same shi da laifin cin amanar budurwarsa Naomi Wanya. Ikehukwu ya karbi N350.000 daga hannun budurwarsa da suka hadu a shafin sada zumunta na Facebook amma sai lamarin ya zama yaudara.

  Alkali A.Y Sanya ya daure Ikechukwu wata shida a gidan yari ko ya biya tara na N50.000.

  Hukumar EFCC a jihar Borno ce ta gurfanar da Ikechukwu a gaban Kotun bayan wacce aka yaudara Naomi ta rubuta takardar koke zuwa hukumar.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta daure wani matashi sakamakon cin amanar budurwarsa a Facebook Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama