• Labaran yau

  Kotu ta adana Dino Melaye har zuwa 11 ga watan Yuni a hannun yansanda

  Wata Kotun Majistare a Lokoja na jihar Kogi ta bayar da umarni a adana Sanata Dino Melaye a hannun yansanda a Lokoja har zuwa ranar 11 ga watan Yuli 2018 .

  An kawo Sanatan ne a cikin motar daukar marasa lafiya na yansanda da misalin karfe 9:17 na safe kuma nan take aka zarce da shi zuwa dakin Kotun.

  Kafin isowarsa Kotun yansanda sun ja daga suka tsaya a wurare masu muhimmancin tsaro a Kotun, haka zalika yan jarida sun yi dafifi a Kotun domin daukar rahotu.

  Ana tuhumar Sanata Dino Melaye da samarwa tare da bayar da kayaki da kudade domin a aikata ta'addanci wanda wasu matasa da aka kama sun riga sun amsa laifi a bincike na yansanda.

  Kafin a kai Sanatan Kotu, an garzaya da shsi zuwa ofishin yansanda na SARS wacce ke kusa da NTA a garin Lokoja.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta adana Dino Melaye har zuwa 11 ga watan Yuni a hannun yansanda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama