• Labaran yau

  Korarren jami'in 'yansanda na SARS ya fada hannu bisa zargin fashin garin Offa

  'Yansanda a jihar Kwara sun kama wani korarren jami'in dansanda bisa zargin kasancewa da hannu a mumunar fashi da makami da aka aikata a Bankuna a garin Offa. An kama Michael Adikwu tare da sauran mutum biyu daga cikin jerin mutane da rundunar ke nema.

  Na'urar CCTV na Bankin ne ya dauki hoton 'yan fashin.

  Rahotanni sun nuna cewa Michael tsohon jami'in dansanda ne wanda ya yi aiki da sashen SARS amma aka kore shi daga aiki bayan an kama shi da laifin karbar kudade daga wadansu 'yan fashi da suka kashe wani mutum kuma ya sake su a lokacin da ayake bincike.

  Daga bisani rundunar ta 'yansanda a jihar Kwara ta sake komo 'yan fashin kuma ta yi wa Michael koran kare daga aikin dansanda kuma aka kai su kurkuku inda Michael ya shafe shekaru uku kawai kuma ya fito.

  Yayin da yake cikin kurkuku Michael ya hadu da wasu manyan 'yan fashi kuma ya shirye wani gungu da suka addabi jihar Kwara da fashi da makami kamar yadda wata majiya ta 'yansanda.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Korarren jami'in 'yansanda na SARS ya fada hannu bisa zargin fashin garin Offa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama