• Labaran yau

  Karanta yadda buhun massara ya makale a kan wani barawo - Hotuna

  Abin mamaki baya karewa a cikin Duniyar nan tamu, wani matashi mai suna Frank Joseph ya fada cikin wani ibtila'i bayan ya gagara saukar da wani buhun massara da ya sata a gidan wata tsohuwa a Nyambwiro. Wannan lamari ya faru a Mbezi a Dar'es Salam na kasar Tanzania.

  Frank dan shekara 23 ya kai kanshi caji ofis na 'yansanda bayan buhun da ya sata na massara mai nauyin kilo 20 ya makale a kanshi.

  Wannan matashi ya yi iya kokarin da zai yi tare da neman taimako da ya wajaba domin a taimaka wannan buhu ya rabu da shi amma lamarin ya gagara. Sakamakon haka Frank ya kai kanshi ga 'yansanda domin su cece shi.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta yadda buhun massara ya makale a kan wani barawo - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama