• Labaran yau

  Karanta abin da Gwamna Yahaya Bello ya ce dangane da kama Dino Melaye

  Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce shi fa ya ga jami'an tsaro suna gudanar da aikin su ne a talabin yayin da aka tambaye shi ra'ayin sa dangane da kama Sanata Dino Melaye da 'yansanda suka yi.

  Bello ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan fitowarsa daga wani taro na APC.

  Gwamna Yahaya Bello da Sanata Dino Melaye mai wakiltar Kogi ta yamma sun dade ba su ga maciji da juna kuma lamari da ya yi sanadin cacan baki da yawan zargin juna a tsakaninsu mutanen biyu wadanda yan jam'iyar APC ne.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta abin da Gwamna Yahaya Bello ya ce dangane da kama Dino Melaye Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama