• Labaran yau

  Kalli yadda kapson tramal ya yi ma wani bahaushe dan okada a jihar Delta

  Wani bahaushe mai aikin okada ya gamu da iftila'i bayan kwayoyin tramal da ya hadiye suka narke sakamakon haka kansa ya juye ya fado daga babur da yake tukawa a jihar Delta.

  Rahotanni sun ce shi dai wannana dan okada ya dauko wasu 'yan mata ne guda biyu, kuma yana cikin tafiya ne sai suka ga ya yi burki kuma ya fadi nan take.

  Jama'a da ke wajen sun matse bakinsa suka dura masa suga bayan dan okadan ya yi ta kokarin yin fada da mutane.Daga bisani kuma aka samo bokitin ruwa aka yi ta kwara masa kafin ya farfado. 
   
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli yadda kapson tramal ya yi ma wani bahaushe dan okada a jihar Delta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama