• Labaran yau

  Kalli yadda aka fede gawar Yarima domin gudanar da binciken asibiti - Hotuna

  Rahotanni sun nuna cewa sakamakon binciken asibiti da aka yi a kan gawar Yarima Kelechi Ineke dan basarake Abaomega ya nuna cewa ya rasa ransa ne yayin da yake tsare a hannun yansanda a Abamomega  na karamar hukumar Onicha a jihar Ebonyi.

  Kwanakin baya mun labarta maku cewa wanda aka kashe a caji ofis ya sami matsala ne da dan wani safeton yansanda da ke aiki a wannan al'umma.

  Sakamakon haka aka kama shi kuma suka azabtar da shi daga bisani kuma ya mutu.Bayanai sun nuna cewa DCO na ofishin na yansanda yana gaba da tare da azazza a kan wata budurwa da suke jayayya da Marigayi Yarima Kelechi, sakamakon haka DCO ya yi amfani da wannan dama domin ya dauki fansa da ya kai ga mutuwar Yariman.

  Tuni DCO, safeton yansanda da dansa suka fada hannun CIID bayan an kama su domin gudanar da bincike.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli yadda aka fede gawar Yarima domin gudanar da binciken asibiti - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama