• Labaran yau

  Gwamnatin tarayya ta haramta shigowa tare da sarrafa syrup mai kodin


  Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta haramta shigowa ko sarrafa maganin mura mai dauke da sinadarine kodin (codiene). Sanarwar ta fito ne daga bakin Ministan lafiya Prof. Isaac Adewole ta hannun daraktan sadarwa na ma'aikatar Mr. Obajide Oshundun ranar Talata a birnin Abuja.

  Wannan ya biyo bayan yadda ake samun yawan karuwar masu amfani da maganin murar ba bisa ka'ida ba a tsakanin matasa ciki har da matan aure. Lamari da ya fi kamari a jihohin arewa.

  Rahotanni sun nuna cewa fiye da kwalabe miliyan 3 ne ake zuka na syrup a kullum tsakanin jihohin Kano da Jigawa kadai.

  Haka zalika Aisha uwargidar shugaba Buhari ta bayyana damuwarta a kan yadda yawan shan syrup ke dada zama barazana a tsakanin matasa. Aisha ta yi wannan bayani ne a shafinta na sada zumunta.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnatin tarayya ta haramta shigowa tare da sarrafa syrup mai kodin Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama