• Labaran yau

  Ba zan ba talakawan Najeriya kunya ba - Shugaba Buhari

  Shuagaba Buhari ya sha alwashi cewa ba zai ba talakawan Najeriya kunya ba. Shugaban ya yi wannan jawabi ne yau yayin wani taro na jam'iyar APC a Dutse na jihar Jigawa inda yake ziyarar aiki na kwana biyu.

  Ya kuma shaida ma 'yan jam'iyarsa cewa yana sane da halin kuncin rayuwa da talakawan Najeriya ke ciki saamakon kuncin tattalin arziki musamman a fannin kayakin masarufi, ya ce yana iya kokarinsa domin ganin talaka ya sami sauki a rayuwarsa.

  Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da shinkafar kasar waje ne domin ta bunkasa noman shinkafa na cikin gida Najeriya domin manoma na gida su amfana.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ba zan ba talakawan Najeriya kunya ba - Shugaba Buhari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama