• Labaran yau

  An kama korarren 'dansanda da ya jagoranci fashin banki a Offa -ISYAKU.COM

  'Yansanda ajihar Kwara sun kama madugun 'yan fashi da makami da suka yi fashi a Bankin garin Offa na jihar Kwara da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama ciki har da jami'an tsaro na 'yansanda.

  Wadanda aka kama sune Kunle Ogunleye 'dan shekara 35 aka Arrow da Michael Adikwu wanda korarren 'dansanda ne mai mukamin kofur.

  An kore Michael Adikwu daga aikin 'dansanda a 2012 bayan ya hada baki da wasu 'yan fashi ya sake su yayin da ake bincike akan wani fashi da makami da ake zargin sun aikata.

  Daga bisani aka gurfanar da Michael Adikwu a gaban Kotu da ta daure shi, amma bayan ya yi shekara uku a gidan Kurkuku sai ya fito daga bisani ya rikide ya zama babban madugun 'yan fashi da makami da ya jagoranci fashi a garin Offa wanda ya yi sandin kashe 'yansanda fiye da 10 tare da fiye da mutum 20.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama korarren 'dansanda da ya jagoranci fashin banki a Offa -ISYAKU.COM Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama