• Labaran yau

  Alkali ya sa an cakume Evans zuwa dakin Kotu bayan ya ki saukowa daga mota

  Fitaccen wanda ake zargi da sace mutane domin garkuwa da su Evans ya jawo 'yarkallo bayan ya ki saukowa daga motar jami'an gidan yari da suka kawo shi babbar Kotun Igbosere da safiyar Litinin 7 ga watan Mayu a garin Lagos domin ci gaba da shari'ar da ake masa.

  Daga bisani Evans ya yi kokarin yin fada da wani ma'aikacin gidan Yari da ya yi kokarin tafiya da shi zuwa cikin dakin Kotun.

  Sakamakon haka Alkalin da ke kula da shari'ar ya yi umarni a shigo da Evans zuwa cikin dakin Kotu da karfi, sakamako haka aka cakume Evans aka daga shi cak zuwa dakin Kotun.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Alkali ya sa an cakume Evans zuwa dakin Kotu bayan ya ki saukowa daga mota Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama