• Labaran yau

  Yansandan jihar Kebbi sun kama mutum 11 da suka kashe jama'a a Bena

  Rundunar yansanda a jihar Kebbi ta kama wasu mutum 11 bisa zargin kashe mutum 5 a garin Bena cikin karamar hukumar Danko wasag. Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi Ibrahim Kabiru ya shaida wa manema labarai haka a hedikwatar yansanda da ke Birnin kebbi ranar Talata.

  Kwamishinan ya ce mutum 11 da aka kama sun shigo ne daga jihar Zamfara suka kashe mutum 5 a garin  Bena

  Ya kara da cewa an kashe mutum 5 ranar 20 da 22 ga wataan Afrilu yayin da aka sace babura 15.
  Haka zalika ya ce mutum 10 daga cikin wadanda aka kama yan jihar Zamfara ne shi kuma ragowar daya dan asalin jihar Kebbi ne amma mazauni jihar Zamfara.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansandan jihar Kebbi sun kama mutum 11 da suka kashe jama'a a Bena Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama