• Labaran yau

  Yansanda sun tsere sakamakon mutuwar dan wani basarake a caji ofis

  Mutuwar wani Yarima Ineke Kelechi dan basaraken garin Abaomege  Eze Ineke a ofishin yansanda a jihar Ebonyi ya yi sandin tashin hankali da ya kai ga kone caji ofis na garin yayin da yansanda da ke aiki a ofishin suka ranta na kare watau suka tsere da gudu kuma sun shiga buya.

  Majiyarmu ta labarta cewa saurayin da ya mutu an same igiya daure a wuyarsa kuma da ransa yansanda suka kulle shi a cikin kurkukun caji ofis na garin na Abaomege, amma sai ga shi an fito da gawar saurayin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansanda sun tsere sakamakon mutuwar dan wani basarake a caji ofis Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama