• Labaran yau

  Yansanda sun je neman Dino Melaye a asibiti, sun kama ma'aikata 2 - Hotuna

  Rahotanni daga birnin Abuja sun ce yansanda karkashin jagorancin kakakin hukumar yansanda Jimoh Moshood sun yi diran mikiya a Asibitin Zankili da ke unguwar Mabushi a Abuja wajen da aka ce Sanata Dino Melaye yana jinya.

  Bayanan farko sun nuna cewa Sanatan ya yi kokarin ya tsare ne bayan yansanda sun kama shi a kan hanyarsu ta zuwa Lokoja.

  An sami hatsaniya a Asibitin bayan yansanda sun kama ma'aikatan Asibitin guda biyu, haka zalika bayanai sun ce yansandan sun gayyaci shuagan Asibiti inda suke neman bayani a kan inda Sanatan yake.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yansanda sun je neman Dino Melaye a asibiti, sun kama ma'aikata 2 - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama