• Labaran yau

  Yan achaba sun yi wa jami'in VIO mugun duka a Abuja

  Wani jami'in VIO a birnin Abuja ya sha dukar tsiya a hannun wasu da ake zargin cewa yan Achaba ne.Jami'in mai suna Mr Abubarkar Eyge ya sha duka a hannun yan achaban ne bayan ya yi kokarin tafiya da wani babur da ake zargi da aikata laifi.

  Sakamakon haka ne wasu matasa yan achaba suka yi gungu suka afka wa jami'in da duka.

  Kakakin hukumar na birnin Abuja Mr. Kalu Emetu ya shaida aukuwar lamarin ranar Talata.ya kara da cewa lamarin ya faru a Area 1 ne na gundumar Garki a birnin Abuja.

  Ya ce yanzu haka maganar na hannun yansanda kuma sun fara bincike a kan lamarin.

  Jami'an VIO 7 ne suka mutu sakamakon shan dan karen duka a hannun yan achaba a birnin Abuja a 2017.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yan achaba sun yi wa jami'in VIO mugun duka a Abuja Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama