• Labaran yau

  Yadda Dino melaye ya yi tsalle daga motar yansanda, ya sami raunuka - Hotuna

  Wani labari daga Abuja ya ce wasu yan daba sun kwace Sanata Dino Melaye daga hannun yansanda a daidai randabawal na Area 1 da ke Abuja bayan wani kwanton bauna da yan daban suka yi wa motoci biyu kirar Hilux wanda ke dauke da Sanatan a kan hanyar su ta zuwa Lokoja domin a gurfanar da Sanatan gaban Kotu.

  Daily trust ta ruwaito cewa jami'an yansanda na SARS ne suke tafe da shi kafin aukuwar lamarin.

  Amma wata majiya ta ce shi Sanata Melaye ne ya yo tsalle da kanshi daga motar kuma ya fado kasa sakamakon haka ya sami raunuka.

  Yanzu dai haka Dino Melaye yana kwance a wani Asibitin Zankli a unguwar Mabushi a garin Abuja inda yake jinya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Dino melaye ya yi tsalle daga motar yansanda, ya sami raunuka - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama