• Labaran yau

  Yadda akwatin gawa ya ki shiga kabari, amma sojoji sun tilasta ya shiga - Hotuna

  Wani abin al'ajabi ya faru a kasar Zambia bayan wani akwatin gawa ya fara tafiyya da kansa  ba tare da an dauke shi ba, wai yana neman wani Maye mai suna Kikondo a gundumar Kaoma.

  Wannan lamari ya kawo rudani tare da haifar da kace nace akan yadda hakan ya kasance.

  Amma daga karshe kwamishinan gundumar na Kaoma Kennedy Mubanga ya shiga cikin lamarin inda ya umarci soji da yansanda suka kama akwatin gawar karfi da yaji kuma suka yi mata rakiya aka saka ta a cikin kabari aka binne ta.

  Dole yansanda suka yi ta harba barkonon tsohuwa kafin daga karshe aka sami sukunin shawo kan lamarin.Wasu matasa da suka harzuka da matakin na jami'an tsaro sun fasa gilashin motar wani dan jarida da yake daukan rahotu a wajen.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda akwatin gawa ya ki shiga kabari, amma sojoji sun tilasta ya shiga - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama