• Labaran yau

  Yadda aka yi yunkurun juyin mulki a Saudiya

  Labarai da suka fito daga TRT sun nuna cewa kasar Saudiya ta shiga zaman zullumi bayan wani yunkurin juyin mulki da ake zargin an yi a fadar Sarki a birnin Riyadh.

  Kafafan yada labaran Amurka sun rawaito cewa an yunkurin juyin mulkin a kasar Saudiyya

  A yayin da aka ji karar fashe-fashen wasu ababe da na bindigogi a gaf da fadar sarkin 

  Saudiyyya,kafafan yada labaran Amurka sun sanar da cewa kwamandan sojojin kasan 

  Saudiyya,Alukas Nepils tare da wasu gungun sojoji sun yi yunkurin hambarar da mulkin sarki Salman.

  Wasu majiyoyin sun rawaito cewa magoyan bayan yarima Talal bin Walid ne suka yi yunkurin juyin mulkin.

  Haka zalika an tabbatar da cewa jirage sun dinka shawagi a sararin samaniyar Riyadh.

  An shaida sarkin Salman bin Abdel Aziz ya nemi mafaka a wani wurin buya,yayin dansa yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ke cikin fada.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda aka yi yunkurun juyin mulki a Saudiya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama